An aurar da mata 150 a rana daya a India

Image caption Mahesh yace yana daukar nauyin aurar da matan ne don taimakon al'umma

Wani attajiri Mahesh Savinda ya aurar da mata 150 a jihar Gujurat a India tare da yin walimar ga daruruwan mahalarta bikin.

Hamshakin dankasuwan ya dade yana daukar nauyin bukukuwan irin wannan aure, a inda ya ke biyan sadakin amaren tare da gudanar da walimar biki a kowacce shekara.

A shekarar 2014 Mahesh ya aurar da mata 111 a inda ya hada musu da kyautar kayan ado da na aikin gida na kimanin rupees 450,000 kimanin dalar Amurka 7,300 ga kowannensu.

Mista Savani yace ya soma daukar nauyin auren ne a shekaru kimanin bakwai da suka wuce bayan da wani ma'aikacinsa ya mutu kwanaki 12 kafin ranar aurar da 'ya'yansa biyu.

Wadanda Mahesh ya ke aurarwa marayu ne wadanda iyalen su ba su da sukunin aurar da su.