Sojan Nigeria sun kutsa dajin Sambisa

Hakkin mallakar hoto Nigerian Army

Runduanar sojan Nigeria tace, ta soma gudanar da farmaki a dajin Sambisa wanda suka ce, shi ne kadai ya rage inda 'yan Boko Haram suke da karfi sosai.

Wata sanarwa daga sojan Najeriyar tace, dakaru sun kutsa cikin dajin na Sambisa, inda suke kawar da sansanonin 'yan Boko Haram da kuma kubuto wadanda 'yan Boko Haram suka sace.

Sanarwar ta kuma ce, yayin samamen an kama 'yan Boko Haram da dama kuma aka lalata makamansu.

Sojan Najeriyar sun ce, dakarun kasa da tallafin sojan sama sun kawar da sananonin 'yan Boko Haram dake Shuari, Adembe, Yerimari Kura, Yerimari Gana, Gonin Kurimi, da kuma Kore da Mainya Kore da kuma Lopere.

A fafatawar da aka yi a Yerimari Gana, an kashe 'yan Boko Haram da dama yayin da wani soja ya ji rauni.

Ana daukar dajin Sambisa a matsayin wani wuri da 'yan Boko Haram suka yi kaka gida.