INEC ta ce zaben Bayelsa bai kammala ba

Hakkin mallakar hoto Channels TV
Image caption INEC ta bayyana zaben jihar Bayelsa dake kudu maso kudancin Najeriya da cewa bai kammala ba.

Hukumar zaben Najeriya, INEC ta bayyana zaben da aka yi na gwamnan jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin kasar da cewa bai kammala ba.

Kazalika, INEC ta soke zaben karamar hukumar Ijaw ta kudu saboda zargin kwace akwatunan zabe da sauran laifukan zabe.

Sai dai ba ta fadi ranar da za a kammala zaben ba.

Hukumar dai ta bayyana sakamakon zaben ragowar kananan hukumomi bakwai na jihar

Jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ta yi marhabin da matakin hukumar zaben, sai dai jam'iyyar APC ta yi watsi da hakan.

Manyan 'yan takarar gwamnan dai su ne gwamna Seriake Dickson na PDP da Timipre Sylva na APC.