Buhari ya tsara kasafin N6tr na 2016

Majalisar ministocin Najeriya ta amince da daftarin kasafin kudin kasar na farko da shugaba Muhammadu Buhari ya yi tun bayan zabensa a watan Maris.

Ministan kasafin kudi a kasar Udoma Udo Udoma, ya ce kasafin kudin na shekarar 2016, ya kai naira triliyan 6, wanda aka samu karin naira triliyan daya da biliyan 500 a kan kasafin 2015.

Ministan ya ce za a aika da kasafin majalisar dokokin kasar domin ta amince da shi.

Mista Udoma ya ce an ware kashi talatin cikin dari na kasafin kudin don gudanar da manyan ayyuka.

An shirya kasafin ne duk da faduwar farashin man fetur wanda ke samar da fiye da kashi 70 cikin dari na kudaden shiga a Najeriya.

Shugaba Buhari ya ce gwamnati na so ta fadada hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasar ta hanyar habbaka aikin gona da hakar ma'adinai.