Buhari ya tsame kansa daga dokar yada labarai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Buhari ya nemi da a yi taka tsan-tsan dangane kudurin dokar yada labarai mai kace-nace

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nisanta kansa daga kudurin dokar yada labarai mai cike da kace-nace wacce masu rajin kare hakkin kafofin yada labarai ke cewa dokar za ta yiwa 'yancin fadin albakacin baki takunkumi a kasar.

A wata sanarwa da shugaban ya fitar ya ce " 'yancin fadin albarkacin baki shi ne kashin bayan mulkin dimukuradiyya a ko'ina a duniya idan babu shi zababbun wakilai ba za su samu damar auna yadda jama'ar ke ji ba game da batun da suka shafi mulki".

Jama'ar a Najeriya sun harzuka kan kudurin dokar da yanzu ake muhawara a kan ta a majalisar dattijai, dokar ta tanadi hukunci a kan duk wanda ya yada labarin karya a kafar yada labarai ta komfuta.

Shugaba Buhari ya yi kira da a kwantar da hankali, ya kuma ce ba zai sa hannu a kan dokar ba, domin ta sabawa tsarin mulkin kasar.

Dokar ta tanadi daurin shekara bakwai a gidan yari ko kuma tarar Naira 4,896,250 ($25,000) ga duk wanda aka samu da laifin yada labarin karya da gangan wanda ka iya kawo barazan ga tsaron kasar ko kuma tunzura jama'a ga kin gwamnati ta hanyar tura sakwanni a na'urar komfuta.