Za a rage fitar da gurbatacciyar iska

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manyan shugabannin kasashen duniya sun halarci taro kan dumamar yanayi a birnin Paris.

Masu bincike sun ce akwai yiwuwar rage iskar da ke dauke da sinadarin Carbon a wannan shekarar, duk da cewar lokaci ne na bunkasar tattalin arzikin kasashe.

Wani hasashen da jami'ar East Anglia tare da kungiyar Global Carbon Project suka yi, ya nuna cewa za a samu raguwa a yawan iskar Carbon da ake fitarwa.

Mai sharhi kan harkokin muhalli na BBC ya ce idan har binciken ya tabbata, toh zai nuna cewa kasashe na iya samun ci gaban tattalin arziki kuma a lokaci guda su rage yawan gurbatacciyar iskar da suke fitarwa.

Masana kimiyya dai sun ce dole iskar da ake fitarwa ta ragu sosai, domin a samu daidaito a yanayin muhalli.

Sun kuma yi kira ga manyan shugabanni a birnin Paris, da su cimma yarjejeniyar da za ta shawo kan dumamar yanayi.

An bukaci Ministocin kasashen, da su cimma matsaya ga yarjejeniyar kafin ranar Alhamis, inda Majalisar Dinkin Duniya kuma za ta yi amfani da duk abunda suka amince a kai ranar Jumma'a.