Burkina Faso: 'Diendere da hannu a kisan Sankara'

Image caption Ana zargin Janar Diendere da hannu a kisan tsohon shugaban Burkina Faso, Thomas Sankara.

An tuhumi jagoran juyin mulkin da aka yi a Burkina Faso da hannu a kisan tsohon shugaban kasar Thomas Sankara.

Janar Gilbert Diendere ne jami'in soji mafi girman mukami da aka tuhuma da hannu a kisan wanda aka yi a shekarar 1987.

Wadansu sojoji ne dai suka kashe Shugaba Sankara, amma har yanzu babu wanda ya san hakikanin yanayin da aka kashe shi a cikinsa.

Har yanzu mutane da dama a Afirka na daukar Thomas Sankara, wanda ake yiwa lakabi da "Che Guevaran Afirka" saboda ra'ayinsa na gurguzu, a matsayin gwarzo.

Zuwa yanzu an tuhumi wadansu jami'an goma da hannu a mutuwar Mista Sankara.