Google ya kaddamar da Wi-fi a Kampala

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kamfanin Google

Kanfanin Google ya kaddamar da hanyar shiga intanet sanfurin Wi-fi a daukacin birnin Kampala na kasar Uganda.

Hakan daya ne daga cikin matakan da kanfani ke dauka na samarwa al'ummomin kasashe masu tasowa hanyoyin sadarwa na internat masu rahusa da inganci.

Birnin Kampala ya kasance na farko a duniya inda wannan tsari zai kafu.

A cikin 'yan shekaru, wani kanfanin intanet ya shinfida wayoyi sardarwa da ake kira ''Optic Fibre'' sama da kilomita dubu takwas a Uganda.

Domin yin anfani da sabon layin sadarwa na intanet na tafi da gidanka na kanfanin Google, kanfanonin kasar masu samar da internat za su biya kudi.

To sai dai Google na fatan ganin masu anfani da intanet za su yi amfani da tsarin cikin sauki idan kanfanonin samar da intanet su ka bude turakun samar da intanet.

To sai dai wasu masu samar da hanyoyin intanet na korafin cewa kanfanin na Google na zuba jari a kasuwar babban birnin kasar da tuni ke da hanyoyin sadarwa, abu mafi dacewa shi ne ya tunkari yankunan karkara wuraren da ake samun matsaloli da hanyoyin intanet.

A cikin watan Oktoba, Facebook ya sanar da yin irin wannan tsari na kara samar da sararin sadarwa na intanet a Afirka ta hanyar anfani da tauraron dan Adam.