"IS na samun taimakon $80m duk wata"

Hakkin mallakar hoto
Image caption IS na samun kudaden ne daga haraji da kwace.

Wani sabon rahoto ya nuna cewar kungiyar IS na samun kudin shiga dala miliyan tamanin a duk wata.

Wani kamfanin da ke sa ido a kan harkokin kudi, IHS, ya ce kungiyar na samun kaso 50 cikin dari na kudaden shigarta daga harajin da ta ke karba a yankunan da ke karkashin ikonta da kadarorin da take kwacewa.

Kamfanin na IHS ya ce IS na samun kaso 43 cikin 100 daga mai da sayar da wutar lantarki da kuma kyaututtuka.

Ya kara da cewa dogaron da kungiyar IS ke yi kan taimakon kasashen waje kadan ne idan aka kwatanta da Al Qaeda.