Za a karawa sojoji wa'adin murkushe Boko Haram

Hakkin mallakar hoto boko haram
Image caption Kungiyar ta Boko haram dai ta kashe dubban mutane.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta karawa sojojin kasar wa'adin da ya dibar musu na murkushe kungiyar Boko Haram.

A kwanakin baya ne dai shugaban ya bai wa sojojin umarnin kawar da kungiyar kafin karshen watan Disambar da muke ciki.

Sai dai a wani taron manyan jami'an rundunar sojin kasar da aka yi a birnin Dutse na jihar Jigawa, Babban Hafsan tsaron Najeriya, Janar Abayomi Gabriel Olonishakin, wanda ya karanta jawabin Shugaba Buhari, ya ambato shi yana cewa a shirye gwamnatinsa take ta kara wa sojojin wa'adi idan suka bukaci hakan.

Kungiyar ta Boko haram dai ta kashe dubban mutane, sannan ta kori miliyoyin mutane daga gidajensu, musamman a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.