'Yan ta'adda ne suka kawo mana hari — Obama

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Obama ya sha alwashin murkushe kungiyar IS.

Shugaba Barack Obama na Amurka ya ce harbe mutane 14 da aka yi a California a makon jiya aiki ne na ta'addanci, sai dai ya ce babu wata shaida da ke nuna cewa wata kungiyar ta'addanci daga wata kasa ce ta shirya shi.

Mista Obama ya sha alwashin ganin bayan kungiyar IS - wacce ta yi ikirarin cewa masu goyon bayanta ne suka kaddamar da harin.

Ya ce, "Barazanar da muke fuskanta a fili take, amma za mu shawo kanta. Za mu lalata kungiyar IS da sauran kungiyoyin da ke kokarin yi mana illa".

Mista Obama ya ce ba da Musulinci Amurka ke yaki, kuma ya bukaci Musulman kasar da su sa hannu a yakin da ake da masu tsatssauran ra'ayin addinin Musulinci.

Ya kuma bukaci majalisar dokokin Amurka da ta bullo da hanyar da za ta sa ya yi wahala ga mutanen da ke cikin jerin wadanda kasar ta hana shiga ko fita daga kasar, su iya sayen bindiga.