An nada Ooni na Ife

Image caption Ooni Adeyeye Enitan Ogunwusi ya yi kira ga Yarbawa su hada kai da sauran 'yan Najeriya.

A Najeriya, dubban mutane ne suka halarci taron bikin nadin sabon sarkin al'ummar kabilar Yarabawa, watau Ooni na Ife, sarautar da ake daukakawa a Kudu maso yammacin kasar.

An nada Adeyeye Enitan Ogunwusi, mai shekaru 40 a watan Oktobar bana, inda ya maye gurbin tsohon sarkin Oba Sijuwade wanda ya rasu a wani asibiti a London, yana da shekaru 85.

Manyan kasa da suka hada da mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, sun halarci taron da aka gudanar a jihar Osun.

An tsaurara tsaro a dandalin taron, inda aka yi ta kide-kide da raye-raye.

Wannan sarautar ta fi kowacce muhimmanci a tsakanin kabilar yarbawan Najeriya.

Kabilar Yarabawa ita ce ta biyu mafi yawa cikin kabilun Najeriya, kuma an yi kiyasin za su kai miliyan 35 a Afrika ta Yamma.