'Yan hamayya sun lashe zaben Venezuela

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jam'iyyar Socialists ta kwashe kusan shekaru ashirin tana shugabanci.

Jam'iyyar hamayya a kasar Venezuela ta lashe galibin kujeru a zaben majalisar dokokin kasar, wacce jam'iyyar Socialists ta Shugaba Nicolas Maduro ta kwashe kusan shekaru 20 tana jagoranta.

Hukumar zaben kasar ta ce jam'iyyar hamayyar ta lashe kujeru 99.

Jam'iyyar Socialists ta lashe kujeru 46, ko da ya ke har yanzu ba a bayyana sakamakon zaben kujeru 22 ba.

Shugaba Maduro ya amince da shan kaye.

Wannan dai shi ne kaye mafi muni da jam'iyyar Socialists - wacce tsohon shugaban kasar Hugo Chavez ya kafa a shekarar 1999 - ta sha.