Schwarzenegger na so a rage cin nama

Hakkin mallakar hoto TriStar Pictures
Image caption Arnold Schwarzenegger mai fitowa a fina-finai kuma tsohon gwamnan California a Amurka

Shahararren mai fitowa a fina-finan Amurka, Arnold Schwarzenegger, wanda aka fi sani da Terminator ya yi kira ga mutane da su rage cin nama.

Terminator ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi a taron da ake yi a kan dumamar yanayi a birnin Paris na kasar Faransa.

Fittacen jarumin kuma tsohon gwamnan jihar California a Amurka ya ce kiwon shanu na daya daga abubuwan da ke haifar da isakar gas mai haddasa dumamar yanayi.

Arnold Schwarzenegger ya ba jama'a shawarar da su koma cin ganye da kayan lambu a kwana daya ko biyu a kowanne mako.

Jarumin ya yi suna a fitowa cikin wasannin motsa jiki, kuma ya tara kwanji.