Tsokaci kan sabon kasafin kudin Nigeria

Hakkin mallakar hoto cbn facebook page
Image caption Tattalin arzikin Nigeria na tsaka mai wuya

Masu sharhi kan tattalin arziki a Nigeria sun soma tsokaci kan kudin da ake sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai kashe a badi, a matsayin kasafin kudi na 2016.

Wasu daga cikinsu na ganin cewa duk da yawan kudin da ke cikin kasafin kudin na shekara mai zuwa, aiwatar da kasafin mai yiwuwa ne idan gwamnati za ta tabbatar da matakan bin kasafin kudin sau da kafa da kuma neman wasu hanyoyin samun kudin shiga dabam da na man fetur.

An yi wannan kasafin kudin da ya zarta kowanne a tarihin kasar ne, a yayin da farashin mai ke kasa da dala 40 kowacce ganga.

A tattaunawar su da wakilinmu na Kaduna, Nurah Mohammed Ringim; Malam Jafar Dabai na makarantar kimiyya da fasaha ta Kaduna ya ce, duk da faduwar farashin mai kasafin na naira Tiriliyan shida, mai yiwuwa ne domin a baya kudaden da a kan samu zurarewa ta wata hanya suke yi.

Dabai yace "Ba za a iya cewa wannan kasafin ya yi yawa ba. Muna ganin cewar wata alama ce da ke nuna cewa za a kara yawan ayyukan da ake yi wa jama'a".

Najeriya dai ta dogara ne kacokan a bisa kudin shiga da take samu a sayar da danyen man a kasashen duniya, to amma faduwar farashin man ya jefa tattalin arzikin kasar a cikin mawuyacin halin.