Yunwa na barazana ga al'ummar Ethiopia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yunwa ta addabi jama'a

Gwamnatin kasar Ethiopia ta yi gargadin cewa mutane fiye da miliyan 10 za su fuskancin yunwa a wata mai zuwa.

Wannan adadin shi ne kaso 10 cikin 100 na al'ummar kasar, wacce ke fuskantar yunwa sakamakon mummunar fari a kasar.

Rabin wadanda lamarin ya shafa kananan yara ne.

A yanzu haka dai gwamnatin kasar da kuma hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya sun soma rarraba abinci a yankunan da damuna bata yi kyau ba, a sassan daban-daban na kasar.

Gwamnatin Ethiopia ta kara adadin mutanen da ke bukatar tallafin abinci daga wata mai zuwa inda aka samu karin mutane miliyan biyu.