Ghana: Za a kara kudin wuta da na ruwa

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Jam'iyyar adawa ta soki gwamnatin Ghana kan karin kudin wuta da ruwa.

Za a kara kudin wutar lantarki da na ruwa a Ghana da fiye da kashi 50 cikin 100 daga mako mai zuwa.

Hukumar da ke kula da wadannan bangarori ta amince da karin kashi 59 cikin 100 na kudin wutar lantarki da kuma tsakanin kashi 69 da 89 cikin 100 na ruwa.

Wata mai magana da yawun hukumar ta ce ba don yawan dauke wutar da ake yi ba da hukumar ta amince da bukatar kamfanonin wutar lantarki na kara yawan kudin wutar da kashi 126.

Ta ce karin zai bai wa masu samar da wutar damar neman rancen kudi ba tare da gwamnati ta shiga tsakani ba.

Jam'iyyar adawa ta New Patriotic Party ta kira wannan mataki da cewa rashin jin kan al'umma ne a kara kudin wuta da ruwa daf da bikin Kirisimeti.