An kwato birnin Ramadi daga hannun IS

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kwato wasu gundumomi na birnin Ramadi daga hannun 'yan IS

Majiyoyin sojojin Iraqi sun shaidawa BBC cewa wani luguden wutar da sojoji suka yi a birnin Ramadi ya sa sun kwato wasu gundumomi daga hannun mayakan 'yan kungiyar IS.

Sojojin sun yi amfani da gadojin tafi da gidanka wajen tsallaka kogin Euphrates kafin su kai hari birnin.

Majiyar ta ce akwai yiwuwar za a kaddamar da harin karshe nan ba da jimawa ba.

Mayakan kungiyar IS sun kwace birnin Ramadi wanda ke da nisan kilomita 120 daga yammacin Bagadaza, tun a watan Mayun da ya gabata.

Sojojin Iraqi da taimakon hare-haren saman da dakarun hadin gwiwa ke kai wa sun yiwa birnin kofar rago na kusan watanni biyar.