Ya ya sunan kungiyar: IS, ISIS, ISIL ko Daesh?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Farfaganda a kan yaki da kungiyar IS

Yayin da hare-hare ta saman da ake kaiwa kungiyar IS mai ikirarin kafa daular musulunci ke zafafa, Farfesa Philippe-Joseph Salazar ya tattauna da BBC a kan farfagandar yakin da ake yi da kungiyar.

"Idan kana da makiyi, to yana da matukar muhimmanci ka san matsayinsa. Ma'anar hakan shi ne dole ka tsaya tsayin daka a kan makiyinka ba tare da ka sauya komai ba, idan ba haka za ka shiga rudani."

"Da ya ke tattaunawa da shirin Newshour na BBC, Philippe-Joseph Salazar, ya ce akwai sunaye daban-daban da ya kamata a rinka kiran 'yan kungiyar da suke a Iraki da kuma Syria da su: ISIS ko ISIL ko Daesh.

Da yake magana a kan kungiyar wadda ta barbazu ko ina a cikin yankin gabas ta tsakiya da Afrika da kuma Asia; Majalisar dinkin duniya da jami'an Amurka suna kiran kungiyar da suna "ISIL".

Ita kungiyar da kanta ba ta amfani da wannan sunan, tun a watan Yunin 2014 a lokacin da ta ayyana kafa daular musulunci, sai ta mayar da sunanta zuwa "IS".

Farfesa Salazar na ganin cewa ya kamata mu rinka amfani da "Khilafa".

Me yasa ba za mu kira su da sunan da suka sanyawa kansu ba? Mun san cewa kalmar Khilafa an santa da bin tsarin siyasa. Mun san yadda kungiyar ta ke da kuma irin halayyarta.

Yaya martanin masu adawa da kungiyar IS ?

A zahiri bamu san yadda ake farfagandar yaki ba. Ba mu mayar da hankali ba a kan yadda ake zafafa hare-hare a kan mayakan IS tun daga makon daya wuce, a yayin da dakarun Amurka tare da na Biritaniya suka zafafa hare-hare a wuraren da 'yan IS suke a Syria.

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Hare-hare ta sama da ake kaiwa kungiyar IS

Kazalika Farfesa Salazar ya yi amanna cewa ya kamata a rubanya hanyoyin da ake bi wajen tunkararsu, yana mai cewa koda yake yaki da kungiyar ya IS ta zamo a ko ina a fadin duniya.

A saboda haka yana ganin cewa akwai bukatar a kara tunani wajen yaki da kungiyar, sannan kuma yana da muhimmanci a rinka sanar da jama'a halin da ake ciki.

Salazar ya ce kamata ya yi a dauki hanyoyi biyu wajen yaki da kungiyar IS, watau ta hanyar farfaganda da kuma amfani da sojoji.

Shin ko akwai damar sansantawa da IS?

Salazar ya yi amanna cewa ba wani rikici da za a samu nasarar warware shi, ba tare da an hada da tattaunawa ba.

A kowanne yaki, akwai yarjejeniya idan an kai wasu matakai. Ya kamata ayi i irin abin da Iran ke yi a halin yanzu.

Ya ci gaba da cewa, koda yake Iran na bin ka'idar yarjejeniyar da aka cimma ta makamashin nukiliya, har yanzu suna da niyyar fito da abin da suka yi niyyar yi.

Farfesa Salazar ya ce IS suna kaddamar da abin da suka ga dama, abin da ya yi amanna cewa ya kamata a tattauna a kai.