Zanga-zanga kan shafukan zumunta a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption 'Yan majaliasar dattawan sun ce ba za su bari 'yan kasar na yin abin da suka ga dama ba.

Masu mu'amala da shafukan sada zumunta a Najeriya na yin zanga-zanga a Abuja, babban birnin kasar domin bijirewa wani kudirin doka da majalisar dattawan kasar ke shirin zartarwa, wanda suka ce zai tauye hakkin fadin albarkacin bakinsu.

A makon jiya ne dai majalisar ta yi wa kudirin dokar karatu na biyu, kuma tana shirin fara sauraren ba'asin jama'a a kansa.

Kudurin dokar ya bukaci "A yi daurin shekara bakwai ko tarar N5m ga duk mutumin da -- da gangan -- ya watsa labaran karya wadanda za su iya yin barazana ga tsaron kasa ko kuma labaran da za su sa 'yan kasa su yi wa gwamnati tawaye".

Haka kuma kudurin ya nemi "A yi daurin shekara biyu ko sanya tarar N2m kan duk wanda ya yi amfani da sakon tes da Twitter, WhatsApp da ma sauran shafukan sada zumunta wajen yin zage-zage da zummar harzuka mutane".

Sai dai masu amfani da shafukan sun kalubalanci 'yan majalisar dattawan, suna masu cewa kudurin dokar "wani yunkuri ne na hana 'yan Najeriya fadin albarkacin bakinsu".

Hadiza Dorayi na cikin wadanda suka yi zanga-zangar, kuma ta shaida wa Abdullahi Kaura Abubakar cewa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sun yi jerin gwano, inda suka yi wa majaliasar tsinke domin neman ka da ta kuskura ta zartar da kudirin.

Wannan batu dai ya sanya masu amfani da shafin Twitter a Najeriya sun kirkiro da maudu'i mai suna #NoToSocialMediaBill, wato "muna kyamar dokar sanyawa shafukan sada zumunta takunkumi".

Shi kansa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ce bai kamata a zartar da kudurin dokar ba saboda ya keta hakkin 'yan kasar na fadin albarkacin bakunansu.

Ya kara da cewa ko da an zartar da shi ba zai sanya masa hannu domin ya zama doka ba.