Gobara ta tashi a ofishin NITEL a Lagos

Image caption A baya-bayan nan ma an yi wata gobara a birnin Lagos da ta hallaka mutane 'yan gida daya.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta tabbatar da gobara da afkuwar gobara a tsohuwar hedikwatar hukumar sadarwa ta kasa NITEL, da ke Lagos a kudancin kasar.

Mai magana da yawun hukumar reshen kudu maso yammacin Najeriya Ibrahim Farinloye ya shaida wa BBC cewa, ba za a iya saurin fadar ko akwai asarar rayuka ko ta dukiyoyi ba.

Sai dai BBC ta gano cewa hukumar kare hakkin masu ajiya a bankuna NDIC, ta koma ginin na NITEL, bayan da ofishin hukumar NDIC din ya yi gobara watanni kadan da suka gabata.

Hukumar NITEL dai ta dade da durkushewa a Najeriya, abin da ake ta'allakawa ga zuwan wayar tafi da gidanka wato GSM, a shekara ta 2001.