Manufofin Buhari na cutar da kasa — PDP

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Jam'iyyar PDP a Najeriya ta ce ce manufofin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma abin da ta kira rashin daukar kwararan matakan tattalin arziki, sun jefa kasar cikin halin ka-ka-ni-kayi.

A wata sanarwa da kakakin jam'iyyar, Cif Olisa Metuh ya fitar, ta ce abin takaici ne 'yadda mulkin Buhari' ke nuna 'rashin tausayi' da kuma mayar da hankali kan tsaka mai wuyar da 'yan Najeriya suke ciki, sakamakon abin da ta kira rashin mayar da hankali wajen inganta tattalin arziki.

Mista Metuh ya ce, "A karkashin wannan gwamnatin, 'yan Najeriya sun yi bikin Sallah mara armashi, kuma ga dukkan alamu bikin Kirisimetin bana, zai zamanto ma fi kuntata da ba a taba yin irinsa ba."

Jam'iyyar PDP ta kara da cewa "abin takaici ne yadda gwamnatin da ta samu mulki ta ikirarin kawo sauyi, a yanzu kuma take wahalar da mutane ta hanyar dabaibaye duk wasu hanyoyin jin dadin rayuwarsu."

A karshe kuma jam'iyyar ta ce tana shawartar gwamnatin da kada ta yi yunkurin kara haraji wanda yin hakan na iya mummunan tasiri a kan talakawan kasar.

Kawo yanzu jam'iyyar APC mai mulkin kasar ko kuma fadar shugaban kasar ba ta mayar da martani ba a kan wadannan zarge-zargen.

Sai dai a baya, shugaba Buhari da kuma jam'iyyarsa ta APC sun yi zargin cewa shekaru 16 da jam'iyyar PDP ta yi a kan mulki, shi ne abin da ya jefa kasar cikin tsaka mai wuya.