An daure wani mai shafin nuna tsaraici a Amurka

Image caption Shafin intanet na "Is Anyone Up"

An daure wani mutun a gidan yari wanda ya bude wani shafin intanet na nuna tsaraicin abokan soyayyar da suka rabu da ake kira "Is Anyone Up", a matsayin wani matakin ramukon gayya.

Mutumin mai suna Hunter Moore, wanda kuma ake wa lakabi da "sarkin nuna tsaraicin mutane don ramuko", ya ce ya bude shafin intanet din ne bayan da buduruwarsa ta yaudare shi.

Sai dai daga baya, Hunter Moore mai shekaru 29, ya kasance yana samun kudade masu yawa ta sanadiyyar shafin da ya bude.

Shafin Is Anyone Up ya na wallafa hotunan tsaraicin mutane, a wasu lokutan ma har da sunayen masu hotunan da bayanan inda suke.

'Yan uwa da iyalan akasarin mutanen da a ke wallafa hotunansu ne suke ganin hotunan.

Wasun su a na cin zarafinsu sosai da kuma tozarta su.

Yanzu dai an yanke wa Moore hukuncin daurin shekaru biyu da rabi a gidan yari, da kuma tarar fiye da dala dubu biyu.

Idan kuma an sako shi daga gidan yarin, za a ci gaba da sa ido a kanshi har na shekaru 3.

Hakan yana nufin, duk lokacin da zai shiga intanet, dole sai jami'in da ke sa mushi ido na tare da shi don ganin abin da zai yi.

Sai dai wasu a Amurka sun yi ta sukan hukuncin da aka yanke mu shi da cewa yayi sassauchi da yawa, inda wasu ke cewa dokokin Amurka ba su dauki laifin yada hotunan tsaraicin mutane don ramukon gayya a matsayin babban laifi ba.