'Yan tawaye sun fara ficewa daga Homs

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A birnin na Homs aka fara zanga-zangar kyamar Assad.

'Yan tawayen Syria sun fara ficewa daga yankin da ke hannunsu na birnin Homs domin yin biyayya ga yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin kasar.

Kungiyar Syrian Observatory for Human Rights wadda ke sa ido kan yarjejeniyar ce ta bayyana hakan, kuma hakan na nufin birnin zai koma hannun gwamnatin kasar.

Mutanen da ke barin birnin za su koma lardin Idlib wanda ke hannun 'yan tawaye.

An taba bayyana birnin Homs,wanda ke tsakiyar Syria, a matsayin "cibiyar juyin juya hali", kuma a can ne aka fara yin zanga-zangar adawa da Shugaba Bashar al-Assad, a shekarar 2011.