Abubuwa 10 da Donald Trumps ya yi amanna da su

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Bangarori da dama sun yi Allah-wa-dai da ra'ayoyin Trump

Mutumin da ke son takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump, ya yi kira da a hana musulmai shiga Amurka, sakamakon mutuwar mutane da dama a wasu harbe-harbe da aka yi a birnin California

Ga kuma sauran manufofin Trump da abubuwan da ya yi imani da su guda 10:

1. Ya ce ya zama wajibi a dunga sa ido kan abubuwan da ke gudana a masallatan Amurka. Trump ya kuma yi amanna cewa ya kamata hukumomin da ke sa ido kan tsaro su dinga yi wa musulmai kofar rago a matsayin wani mataki na yaki da ta'addanci, yana mai cewa bai damu ba idan har wasu za su kalli wannan lamari a matsayin abin da bai kamata ba a siyasance.

2. Amurka ta dinga samo bayanai daga mutane ta hanyar gana musu azaba wajen nutsar da su a ruwa da kuma sauran manyan hanyoyin tuhuma a kokarinta na yaki da kungiyar IS.

3. Trump zai tarwatsa tare da rugurguza kungiyar IS. Ya yi ikirarin cewa babu wani dan takara da zai zama mai tsauri a kan kungiyar IS kamar sa kuma zai raunana karfin 'yan ta'addan ta hanyar katse hanyoyin da suke samun man fetur.

4. Yana so ya gina babbar katanga tsakanin Amurka da Mexico domin ajiye 'yan ci ranin da ba a yi musu rijista ba da kuma 'yan ci ranin Syria. Mista Trump yana ganin cewa yawanci 'yan Mexico da ke zuwa Amurka masu aikata miyagun laifuka ne. "Suna shigowa da kwayoyi, suna shigowa da mugayen laifuka kuma suna aikata fyade," a cewar Trump.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Trump yana da ra'ayin saka takunkumin shiga Amurka.

5. Ya ce dole ne a tabbatar an mayar da kimanin 'yan ci rani miliyan 11 kasashensu, wadanda suke zama a Amurka ba bisa ka'ida ba. An yi Allah-wa-dai da wannan ra'ayi nasa a matsayin abin da ake kallo da kin jinin baki wanda kuma zai jawo kashe makudan kudi. BBC ta kiyasta cewa za a kashe dala biliyan 114 kan hakan. Zai kuma kawo karshen damar zama dan kasa a dalilin haihuwa, wani mataki da ke bai wa 'ya'yan 'yan ci ranin da ke zaune a kasar ba bisa ka'ida ba damar zama 'yan kasa, in dai har an haife su ne a kasar ta Amurka.

6. Zai kulla kawance mai kyau tsakaninsa da Vladmir Putin. A wata hira da ya yi da tashar CNN, Mista Trump ya ce Mista Putin da Mista Obama sun ki jinin juna ne ta yadda har suka kasa sasantawa, "Amma ni kam tabbas zan gyara dangantaka tsakanina da shi. Kuma bana tsammanin da zaka samu irin matsalolin da kake fuskanta a yanzu." In ji Mista Trump.

7. Za a kalubalanci China a kan abubuwa da dama domin a yi huldar kasuwanci tsakaninta da Amurka ba cuta ba cutarwa. Ya ce idan har aka zabe shi zai hana China rage darajar kudinta, zai kuma tursasa ta daukar muhimman matakan inganta muhallinta da kuma sha'anin ma'aikatan kwadago.

8. "Sauyin yanayi bangare ne na yanayi kawai." A yayin da Trump ya yi amanna cewar samun ingantacciyar iska da tsaftataccen ruwan sha suna da matukar muhimmanci, ya yi watsi da kimiyyar sauyin yanayi da cewa hanyar yaudara ce kawai.

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Bangarori da dama sun yi Allah-wa-dai da ra'ayoyin Trump.

9. Trump ya kuma yi amanna cewar da a ce Saddam Hussein da Muammar Gaddhafi suna kan mulki har yanzu, da duniya ta zauna lafiya. Trump ya shaida wa CNN cewa ya yi imani yanayin da Libya da Iraki ke ciki a yau ya fi muni fiye da lokacin da suke karkashin wadancan masu mulkin kama karyar.

10. Ya kuma ce shi mutum ne mai matukar kirki. A wani littafi da ya rubuta a baya-bayan nan mai suna "Crippled America", Trump ya ce "Ni mutum ne mai kirki, ku yarda dani. Ina alfahari da kaina na zamowa mutumin kirki amma kuma ina matukar son na ciyar da kasata gaba fiye da yadda take a yanzu."