'Burundi za ta shiga yakin-basasa'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Nkurunziza ya sake tsayawa takara duk da adawar da aka yi kan hakan.

Mai bai wa Majalisar Dinkin Duniya shawara na musamman kan hana kisan-kare-dangi, Adama Dieng, ya yi gargadin cewa Burundi za ta fada cikin yakin-basasa idan ba a daina kashe-kashen da ke da alaka da siyasa ba.

Adama Dieng ya ce dakarun gwamnati da na 'yan tawayen kasar na yin amfani da kabilanci da manyan makamai domin cimma muradunsu a rikicin kasar.

Ya ce yana fargabar bangarorin da ke yaki a kasar ta Burundi za su yi watsi da yarjejeniyar da aka sanya wa hannun a Arusha a shekarar 1993 kan zamna lafiya a kasar.

A cewarsa, idan hakan ya faru kasar za ta iya fadawa mawuyacin halin da ba ta taba shiga ba.