Kamaru ta dawo da 'yan gudun hijira 18,000

Hukumomi a Najeriya sun bayyana cewa zuwa yanzu jamhuriyar Kamaru ta taso keyar 'yan Najeriya fiye da 18,000 zuwa kasarsu, kuma ana ci gaba da koro 'yan Najeriyar daga Kamaru.

Tarzomar Boko Haram ce ta raba mutanen da muhallansu inda suka shiga kasar ta Kamaru domin neman mafaka.

Alhaji Sa'adu Bello, shi ne jami'in tsare-tsare na Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa a Najeriya NEMA, mai kula da jihar Adamawa da ke iyakar Najeriyar da Kamaru, inda nan ne ake jibge 'yan gudun hijirar, ya kuma shaida wa BBC cewa tun a watan Agustan 2015 ne suka samu labarin taso keyar 'yan kasar da Kamarun ke yi.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ya kara da cewa basu san yawan 'yan gudun hijirar Najeriyar da suka rage a Kamarun ba, saboda jami'an Kamarun ba sa tuntubarsu a hukumance kan wannan batu.

Tun lokacin da hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa a arewa maso gabashin Najeriya ya ta'azzara ne, mutanen yankin suka fara gudun hijira zuwa kasashe masu makwabtaka kamar Kamaru da Chadi da Nijar.