Dokpesi ya musanta tuhumar EFCC

Hakkin mallakar hoto AIT
Image caption Ana tuhumar Raymond Dokpesi da badakalar karbar hanci.

Shugaban hukumar talbijin ta AIT, Mista Raymond Dokpesi ya musanta tuhume-tuhumen da ake masa guda shida na zargin karbar hanci da rashawa.

A ranar Laraba ne Mista Dokpesi ya bayyana a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Ya kuma kara da cewa duk tuhume-tuhumen da ake yi masa ba gaskiya bane.

Daya daga cikin tuhumar da ake masa ita ce zargin kamfaninsa da karbar naira biliyan 2.1 daga ofishin tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro don yin kamfe na takarar shugabanci kasa na jam'iyyar PDP, a kafafen yada labarai.