Masu kutse sun shiga cikin shafin Independent

Kwararu sun ce masu kutse sun saka wata manhaja a cikin shafin jaridar The Independent da ke yin llla ga kwamfutar masu shiga cikin shafin.

Masu bincike daga Trend Micro sun gano cewar masu kutse sun shiga cikin shafin inda suka wata manhaja da ake kira Malware a cikin kwamfar mutane.

Jaridar The Independent ta ce ta cire dukannin talace talacen da ta saka a cikin shafin ya yinda ta ke gudanar da bincike.

" Alamu na nuni da cewa an saka manhajar a cikin sanshin tala na shafin." a cewar kakakin jaridar The Independent.

Sai dai jamiin ya ce wani sashi ne da ba kasafai ya ke amfani da shi ba aka saka manhajar.

Sai dai a cewar kamfanin Trend Micro tun a watan nuwamba bara ne aka saka manhajar a cikin shafin.

Kamfanin ya kuma ce sai da ya ankarar da jaridar a ranar Talata amma haryanzu matsalar ba ta sauya zani ba.