Shugaban Tanzania yana kwashe shara

Image caption Shugaba Magafuli yana kwashe shara a birnin Dar Es Salaam

Sabon shugaban kasar Tanzaniya John Magufuli, ya bi sahun daruruwan mazauna babban birnin kasar Dar es Salaam, wajen gangamin tsaftace muhalli.

Mista Magufuli ya share tare da kwashe datti a kan titi a wani bangare na umarnin da ya bayar na maye gurbin bukukuwan ranar samun 'yancin kai, da tsaftace muhalli.

Wakilin BBC ya ce ana kallon wannan yunkuri a wata alama ta alkawarin da shugaban yayi na kawo karshen karbar hanci da rashawa.

Rahotanni sun ce dubban mutane ne suka aiwatar da aikin tsaftar muhallin a kasar ta Tanzaniya.

A watan da ya gabata ne, Mista Magufuli ya soke bukukuwan tunawa da ranar samun 'yancin kai da ake yi, wanda yawanci ke hadawa da faretin sojoji, yana mai cewa zai zama "abin kunya" a kashe makudan kudade a yayin da kasar ke fama da annobar cutar amai da gudawa.