APC ta rabe gida biyu a Kaduna

An samu baraka a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna da ke arewacin Nigeria.

Barakar ta kunna-kai ne yayin da wasu gaggan 'ya'yan jam'iyyar suka fito fili suna kalubalantar gwamnan jahar, Nasiru El Rufai, wanda suke zargi da kokarin kassara jamiyyar.

A cewarsu, gwamnan ya hana zaben shugabanin jam'iyyar, da kuma wasu tsare-tsaren gwamnatinsa da suke ce na ja wa jam'iyyar bakin-jini.

Sai dai magoya bayan gwamnati, a nasu bangaren sun musanta wadannan zarge-zarge.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ga rahoton da Nurah Muhammed Ringim ya aiko mana da Kaduna