Fernandez ta nemi 'yan Argentina su yi tawaye

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cristina Fernandez de Kirchner ta ce gwamnatinta ta taka rawar gani.

Shugabar Argentina mai barin-gado, Cristina Fernandez de Kirchner ta bukaci al'umar kasar da su fita su yi zanga-zanga don kwatar hakkinsu idan suka ga cewa sabuwar gwamnatin kasar da ke fara aiki yau din nan ta bijire musu.

A wani jawabi mai sosa rai, inda ta yi bankwana da dubban magoya bayanta, Crishtina Fernandez ta kare gwamnatinta da kuma nasarorin da ta samu wajen inganta tattalin arzikin kasar.

Ta ce, "Mun bar wa duniya abin misali cewa ba a kau da ido ga zalunci a Argentina, kuma ba ma bukatar wata kotun kasa da kasa ta mamaye mana tarihinmu".

Sabuwar gwamnatin kasar dai za ta gaji matsaloli, ciki har da hauhawar farashi, da karancin kudi a asusun kasashen waje.