Za a miƙa wa Nigeria 'yan Boko Haram 500

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Twitter
Image caption Mayakan Boko Haram sun hallaka dubban mutane

Mahukunta a jamhuriyar Nijar sun amince za su mika wa Najeriya wasu fursunoni 500 'yan Boko Haram.

Hukumomin Nijar din dai sun dauki wannan matakin ne da nufin rage cunkoso a gidajen yarin kasar.

'Yan Boko Haram na tafka ta'asa a kasashen da ke makwabtaka da Najeriya kamar Nijar da Chadi da kuma Kamaru.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane sannan wasu miliyoyi suka rasa muhallansu.

Kasashen tafkin Chadi sun kafa runduna ta musamman wacce za ta yaki kungiyar Boko Haram inda suka sha alwashin girke dakaru fiye da 8,000.

Gwamnatocin kasashen da rikicin Boko Haram ke addaba suna ci gaba da aiki tare domin ganin sun murkushe mayakan kungiyar.