An tsawaita taro kan sauyin yanayi

Kasashen  duniya da matsalar sauyin yanayi ke yi wa illa Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasashen duniya da matsalar sauyin yanayi ke yi wa illa

Wakilai a taron da ake yi a kan sauyin yanayi a Paris sun tsawaita tattaunawar da suke yi da nufin cimma yarjejeniya zuwa ranar Asabar.

Hakan na nufin an gaza cimma matsaya da za ta sa a kammala taron ranar Juma'a.

Wakilan sun kashe daren Laraba da Alhamis domin daidaitawa a kan bambance-bambancen da suka samu game da wani daftari.

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, ya ce lokaci ya yi na cimma yarjejeniya.

Amma shugabar hukumar da ke kula da yanayi ta majalisar dinkin duniya, Christiana Figueres, ta ce da sauran aik a gaba saboda a ganinta daftari yana da rauni, saboda bai tabo dukkan batutuwa ba.