Kotun Indiya ta wanke Salman Khan

Image caption Salman Khan ya taka wasu mutane da motarsa, lamarin da ya yi sanadiyar ajalinsu.

Wata babbar kotun Indiya da ke Mumbai ta wanke dan wasan fim din kasar Salman Khan daga laifin kisan kai.

A watan Mayu ne wata karamar kotu ta sami Salman Khan da laifin taka wasu mutane da motarsa a shekarar 2002, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsu.

Karamar kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekara biyar a gidan yari bisa laifin tukin ganganci da kisan kai.

Sai dai dan wasan fim din ya daukaka kara, lamarin da ya kai ga babbar kotun ta wanke shi.

Kotun ta ce mutanen da za su bayar da shaida kan lamarin sun mutu, don haka ba ta da tabbacin ya aikata laifukan.

Ga alama masu gabatar da kara za su daukaka shari'a kan wannan hukunci.

Salman Khan na daya daga cikin 'yan wasan fim din Indiya da suka fi farin jini a duniya.