An bankado mutum 682 da ke kallon hotunan yara na batsa

Hukumar binciken miyagun laifuka ta Birtaniya ta ce an kama sama da mutum 680 a cikin watanni tara da suka wuce, wadanda ake zargi da sauke hotunan batsa na kananan yara ta intanet.

'yan sanda dai ba su taba kama sama da kashi casa'in bisa dari na mutanen da aikata irin wannan laifin a baya ba, yayin da mutum 104 daga cikinsu ke rike da wasu mukaman gwamnati, har ma mutum 32 na alaka da bangaren ilimi.

Binciken dai ya gano cewa yara 399 na fuskantar hadari sakamakon wannan kamen.

An dai yi amfani da 'yan sanda 40 wajen yin kamen a fadin Birtaniya, inda aka binciki wurare 600, aka kuma kama mutum 682 tare da tuhumar mutum 147 a gaban kuliya.

'yan sanda na amfani da na'urar kididdigar hotuna wajen yin kamen

Simon Bailey na Norfolk Constabulary shi ne babban jami'in 'yan sanda da ya jagoranci binciken, kuma ya ce 'yan sanda sun yi kokarin kama mutanen da suka fahinci cewa suna hadari sosai ga rayuwar yara.

Ya ce " kwamfutar da ake amfani da ita jin ta ya fi ganin ta, sai dai na'urar kididdigar hotunan tana da tasiri sosai."

Na'urar dai tana da kunshe da dukkan hotunan yaran da aka gudanar da bincike a kan su

A shekarar 1990 an yi tsammanin cewa irin wadannan hotunan da ke tsakanin jama'a ba su wuce 7,000, amma a wani farmaki guda, 'yan sandan bincike sun kama hotunan miliyon biyu da dubu dari biyar a cikin kumfuta daya.

Ana dai fatan cewa wannan na'urar za ta taimaka wajen gaggauta gudanar da bincike tare da kama miyagun mutane, kasancewar kananan yara na bukatar kariya.