'Jonathan ya ci amanar 'yan Nigeria'

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Buhari ya zargi Jonathan da cin amanar da 'yan Najeriya suka dora a kansa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zargi tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan da cin amanar 'yan Najeriya a kan batun sayo makaman da za a yi amfani da su wajen yaki da Boko Haram.

Shugaba Buhari ya yi wannan zargi a lokacin da ya hada wa 'yan majalisar wakilan kasar walima ranar Laraba da maraice a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ya ce abin takaici ne yadda aka kashe biliyoyin kudi domin sayen makaman da, a karshe, ba a saya ba.

Muhammadu Buhari ya kara jaddada matakan da ya ce ya dauka domin kawo karshen kungiyar Boko Haram, yana mai cewa "lokacin da muka zo, mun cire manyan soji sannan muka nada sababbi wadanda muka sanya wa wa'adin da za su kawar da kungiyar".

A cewarsa, "Babban burinmu shi ne mu dawo da dukkan yankunan kasar nan a karkashinmu, sannan mu san yadda za mu inganta rayuwar mutane".

Kawo yanzu dai, tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan, bai ce komai ba kan zargin da Shugaba buhari ya yi masa.

Na bai wa Dasuki kudin da Abacha ya sace

Image caption Okonjo Iweala ta ce ta bai wa Dasuki N63 domin yaki da 'yan ta'adda.

Amma ministar kudi a karkashin shugabancinsa, Ngozi Okonjo Iweala, ta ce ma'aikatarta ta mikawa tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara kan tsaro, Kanar Sambo Dasuki N63bn domin sayen makamai daga cikin kudaden da gwamnati ta kwato, wadanda ake zargin gwamnatin marigayi tsohon shugaban mulkin sojin kasar, Janar Sani Abatcha.

Tuni dai hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya, EFCC ta tuhumi Kanar Sambo Dasuki da laifukan da suka danganci almundahana da halasta kudaden haramun a gaban kotu.

EFCC ta kuma tuhumi tsohon gwamnan jihar Sokoto, Dalhatu Bafarawa da mai gidan talabijin na AIT, Raymond Dokpesi, da laifin aikata irin wadannan laifuka a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

EFCC dai ta kama mutanen ne bisa zargin karkatar da kudade fiye da N2.1bn wadanda ke cikin kudaden da aka ware domin sayen makaman da za a yi amfani da su wajen yaki da 'yan kungiyar Boko Haram.

Sai dai dukkan mutanen da ake tuhuma sun musanta zarge-zargen da akeyi musu.