Muhammad Ali ya caccaki Donald Trump

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Muhammad Ali ya ce ya kamata `yan siyasa su dinga amfani da matsayinsu wajen kyautata fahimtar addinin Musulunci.

Tsohon zakaran damben duniya, Muhammad Ali, ya mai da martani ga mai neman takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump dangane da furucin da ya yi cewa ya kamata a haramta wa Musulmi shiga Amurka.

Zakaran damben dai bai fito fili ya kama sunan Donald Trump ba, amma ya ce ya kamata 'yan siyasa su dinga amfani da matsayinsu wajen kyautata fahimtar addinin musulunci.

Mista Donald Trump dai ya ce ba zai fasa aniyarsa ta neman tsayawa takara ba, duk kuwa da matsin-lambar da yake fuskanta cewa lallai ya janye, bayan kalaman da ya yi cewa a haramta wa Musulmai shiga Amurka, furucin da ya sa al'umar duniya yin tir da shi.

Kusan mutum dubu dari biyu da hamsin ne suka sanya hannu a kan wata wasikar koke, wadda ta bukaci a hana wa Mista Trump shiga Biritaniya.

Wani abokin hamayyar Mista Trump din, wato Gwamnan jihar Ohio John Kasich, ya ce bai kamata mutane su dinga sauraron kalaman Mista Trump din ba.

Ya ce, "Wannan ba abu ne da zai hada kan Amurkawa ba. Kada jama'a su saurari wannan furucin, saboda wannan ba dabi'armu ba ce".

Tuni dai wasu manyan kantuna da dama a yankin Gabas-ta-tsakiya suka haramta sayar da kayan da kamfanin Mista Trump din ke samarwa.