Karya ta ba wa Netanyahu kunya

Image caption Karya ta kunyata bakin Netanyahu

Karyar firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu mai suna "Kaiya" ta ja masa abin kunya.

Karyar ta ciji baki a wajen wani taro da ya shirya a gidansa.

Kaiya ta ciji wani dan majalisar dokoki da kuma mijin mataimakiyar ministan harkokin wajen kasar.

Ba a yi wata-wata ba iyalan Netanyahu suka dauke karyar daga wajen suka shiga da ita cikin gida aka boyeta.

A baya baki da dama na zuwa gidan Firaministan, amma ba bu wani lokaci da karyar ta taba kai wa wani hari.