Kisan Kiyashi: An kama Ntaganzwa a Rwanda

Hakkin mallakar hoto wiki
Image caption Kisan kiyashi a Rwanda ya janyo mutuwar dubban mutane

Majalisar dinkin duniya ta ce jami'ai a Jamhuriyar dimokradiyyar Kongo sun kama, Ladislas Ntaganzwa, mutumin da ake zargi da hannu a kisan kare-dangin da aka yi a Rwanda.

Yana daya daga cikin mutane tara da majalisar ta dinkin duniya ke nema ruwa-a-jallo.

Har yanzu ana ci gaba da neman sauran.

Babban mai gabatar da kara na kotun hukunta mutanen da suka laifukan kare-dangi a Rwanda, Mai shari'a Hassan Bubacar Jallow, ya sanar da kamun Ntaganzwa ga 'yan jarida a hedikwatar majalisar dinkin duiya da ke New York

Ana zarginsa da aikata laifukan kisan kare-dangi da kuma keta hakkin dan adam a kan kisan sama da mutane 20,000 'yan kabilar Tutsi.

Majaliasar dai ta sanya tukwucin dala miliyan biyar kan duk wanda ya taimaka mata ta kama shi.

Ma'aikatar tsaron Amurka tana zarginsa da kasancewa daya daga cikin mutanen da suka kitsa kisan kare-dangin da aka yi a yankin Butare da ke kudancin Rwanda.