Kotun India ta wanke Salman Khan

Image caption A yanzu hankalin Salman ya kwanta

Wata Kotu a birnin Bombay ta wanke tauraron fina-finai na Bollywood, Salman Khan daga hukuncin daurin shekaru biyar, da wata karamar kotu ta yanke masa, bisa zargin kashe wani mutum a lokacin yana tuka mota a shekara ta 2002.

A cikin watan Mayu ne, karamar kotun ta samu Mr Khan da laifin kisan kai bada niyya ba, a lokacin yana tuka mota a cikin yanayi na maye.

Tun a lokacin aka bayar da belinsa saboda ya daukaka kara.

Babbar kotun a hukuncinta, ta ce tun da shaida a shari'ar ya rasu, babu yadda za a iya amincewa da wannan shaidar da ya bayar.

Salman Khan na daga cikin manyan taurarin fina-finai a kasar India.