Boko Haram ta kashe mutane 8 a Kamaru

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An ceto mutane da dama daga hannun 'yan Boko Haram.

Wasu mahara da ake zargi 'yan Boko Haram ne sun kashe akalla mutane takwas a harin da suka kai lardin arewa mai nisa na Kamaru ranar Juma'a da asuba.

Hukumomi sun ce harin, wanda 'yan kunar bakin wake suka kai a garin Kolofata, ya jikkata mutane 21.

Sun kara da cewa 'yan kunar bakin waken na cikin mutanen da suka mutu.

A makonni biyun da suka wuce dai, sojojin Kamaru da ke Kolofata, sun dakile hare-haren da kungiyar ta Boko Haram ta yi yunkurin kai wa.