An cimma matsaya kan sauyin yanayi

Hakkin mallakar hoto Getty

Rahotanni daga birnin Paris na kasar Faransa na cewa mahalarta taro a kan sauyin yanayi sun cimma matsaya a kan daftarin yarjejeniyar da za su sa masa hannu, bayan sun kwashe makwanni biyu suna gagganawa.

Idan an jima ne za a gabatar wa ministoci daftarin.

Wakilai daga kasashen duniya 190 ne dai suka bata-hankalin-dare don cimma wannan yarjejeniyar.

Tun da farko dai shugaban Amurka, Barak Obama ya ya yi magana da takwaransa na kasar China, Shi Jinping da nufin shan-kansa domin a cimma yarjejeniya.

Wannan daftarin dai shi zai kasashen yarjejeniyar kasa da kasa ta farko kan rage hayaki mai gurbata muhalli, idan kasashen duniyar suka amince da daftarin.