An kai wa masaukin baki hari a Kabul

Hakkin mallakar hoto b

Mayakan kungiyar Taliban sun kai hari a wani masaukin baki na yan kasashen waje a birnin Kabul.

An kashe wani jami'in 'yan sanda na kasar Spaniya a cikin harin , da aka soma da fashewar bam a cikin wata mota.

Rahotanni farko sun ce watakila ofishin jakadancin Spaniya ne mayakan su ke son su kai wa hari , sai dai jami'ai sun musanta haka.

Wadanda suka shaida lamarin da idanunwansu sun ce an dinga jin karar harbe harben bindiga bayan sa'oi da kai harin.

Hukomomi a kasar Afghanistan din sun ce watakila akwai ragowar maharan a wurin.