Kotu ta goyi bayan dakatar da Platini

Hakkin mallakar hoto Rianovosti
Image caption An dakatar da Michel Platini ne na tsawon kwanaki 90, bisa zargin karbar hanci.

Shugaban hukumar kwallon kafar Turai, UEFA, Michel Platini, bai yi nasarar sauya dakatarwar da hukumar kwallon kafar duniya FIFA ta yi masa na kwana 90 a kotu ba.

Platini ya daukaka kara a kotu, inda ya nema da a dage dakatarwar da aka yi masa, amma kotun dake sauraron kararraki kan wasanni ba ta bayar da damar hakan ba.

A watan Oktoban bana ne dai Fifa ta dakatar da Platini mai shekaru 60, tare da shugaban na FIFA, Sepp Blatter daga shiga harkokin wasanni, bisa zargin laifin ayyukan karbar hanci.

Dukkanninsu dai sun musanta zargin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.