An zargi Saudiyya da kai hari a Yemen

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Amnesty International ta yi zargin cewa Saudiyya ta lalata makarantu sama da dubu daya a Yemen.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta zargi kasar Saudiyya da kai hari kan makarantu a kasar Yemen da gangan.

Kungiyar ta bayyana cewa daga lokacin da Saudiyya ta fara kai hari a kasar Yemen, a watan Maris din da ya wuce zuwa yanzu an lalata makarantu sama da dubu daya.

A wani sabon rahoto, kungiyar ta bukaci Amurka da Birtaniya da su dakatar da sayar wa Saudiyya makamai, saboda a cewar kungiyar ana amfani da makaman ne wajen taka dokokin kasa da kasa a Yemen.

Wakilin BBC ya ce ana zargin dakarun Saudiyya da na 'yan tawayen Yemen da Iran ke goya musu baya da aikata laufukan yaki.

Sama da mutum dubu sittin ne dai suka halaka a rikicin.