An tuhumi mutane 25 da yin ridda a Sudan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana dai zargin mutanen ne da kin amincewa da hadisan Annabi Muhammad (SAW).

Wani alkali a kasar Sudan ya tuhumi wasu mutane 25 da laifin yin ridda, wato fita daga addinin Musulunci, laifin da ka iya zama na hukuncin kisa a tafarkin Shari'ar Musuluncin kasar.

Ana dai zargin mutanen ne da kin amincewa da hadisan Annabi Muhammad (SAW), amma lauyoyinsu sun ce duk da haka ba su fita daga musulunci ba tun da sun gaskata Alkur'ani.

Wata ruwayar, wadda ba a tabbatar da ita ba, ta ce mutanen sun ce suna da alaka da kungiyar Boko Haram wadda ta yi mubaya'a ga kungiyar IS.

A bara ma dai, kasar Sudan ta shiga bakin duniya lokacin da aka yanke wa wata mata mai suna Maryam Ibrahim hukuncin kisa, bayan ta yi ridda, ta koma addinin Kirista, amma daga baya an juya hukuncin, kuma a halin da ake ciki ta koma Amurka da zama.