Mugabe ya yi katobara

Shugaba Robert Mugabe
Image caption Shugaba Robert Mugabe

Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe ya sake yin wata kwaba, inda ya karanta wani jawabin da ba shi da alaka da wani taron ya halarta.

Shugaba Mugabe ya karanta jawabin ne a wajen taron shekara-shekara na jam'iyyar Zanu-PF mai mulkin kasar, kuma sai da ya ci kusan rabin minti yana karanta jawabin kana aka sauya masa da jawabin da ya dace da taron.

A watan Satumban da ya wuce ma, shugaba Mugaben ya karanta wani tsohon jawabi a majalisar dokokin kasar, wanda ya taba karantawa a baya, kimanin wata guda.

A jawabinsa na taron jam'iyyar Zanu-PF din, Mista Mugabe ya bukaci 'ya'yan jam'iyyar da su daina fada su-ya-su a kan wanda zai gaje shi wajen mulkin kasar ta Zimbabwe.