Za a gina gada mafi tsawo a Bangladesh

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Za a gina gada mafi girma a Bangladesh

Firaministan Bangladesh, Sheikh Hasina, ya sanar da shirn fara gina babbar gadar da ta ratsa kogi a kasar.

Za a gina Gadar mai nisan kilomita shida wadda ta ratsa kogin Padma ne domin hada babban birnin kasar Dhaka da bangaren kudancin kasar.

An kiyasta cewa mutane miliyan talatin da ke yankin ne za su amfana da gadar idan an kammala ta.

A yanzu haka, duk masu son tafiya wani waje da ya ratsa ta kogin, za su rinka amfani ne da jiragen ruwa ko kwale-kwale.

Ana kyautata tsammanin kammala gina gadar a shekarar 2018.

A shekarar 2012 bakin duniya ya tsame kansa daga aikin gina gadar saboda batun cin hanci da rashawa.

Yanzu haka gwamnatin Bangladesh ce ke daukar nauyin ginin gadar wadda za ta ci kudi dala biliyan uku.