Ana tsintar gawawwaki a Burundi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana kashe mutane a Burundi

An samu gawar mutane a kalla talatin da hudu da aka harbe har lahira a kan titunan Bujumbura babban birnin kasar Burundi.

Wani wakilin BBC a birnin ya ce wannan shi ne adadi mafi yawa na mutanen da aka kashe a dare guda.

An kuma samun wasu gawawwakin ashirin da daya a gundumar Nyakabiga, sannan aka sake samun wasu gawawwakin goma sha uku a Musaga.

An dai kashe mutane fiye da dari biyu da hamsin tun daga watan Aprilun da ya gabata, bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya sanar da batun sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na uku.

Kasashen duniya sun gargadi Burundi a kan cewa kada ta samu kanta cikin mummunan rikici sakamakon matakin da shugaban kasar ya dauka.